Zulum ya sake ziyartar waɗanda harin Ngoshe ya rutsa da su
[ad_1]
A karo na biyu, Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sake kai ziyarar jaje ga mutanen da harin Ngoshe ya shafa, waɗanda a halin yanzu suke zaune a matsayin ’yan gudun hijira a garin Pulka.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Asabar a makarantar firamare ta Pulka Central, inda mazauna Ngoshe da suka rasa matsugunansu ke cikin mawuyacin hali.
Aminiya ta ruwaito cewa an kai harin ne a ranar 4 ga watan Maris, lokacin da ’yan ta’adda suka afka wa garin Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa daga gidajensu cikin firgici.
Zulum ya bayyana cewa ziyarar hanya ce ta ƙarfafa goyon bayan gwamnati ga waɗanda abin ya shafa, tare da jawo hankalin masu ruwa da tsaki kan batun tsaro a yankin.
“Babban dalilin da ya sa muke nan shi ne don jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar musu cewa gwamnatin tarayya da ta Jihar Borno za su ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a Gwoza da kewayenta,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto mutanen da har yanzu suke hannun ’yan ta’adda.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnati za ta sake gina kayayyakin more rayuwa da suka lalace, tare da tallafa wa mazauna da suka rasa matsuguni domin komawa gidajensu cikin aminci a Ngoshe.
Haka kuma, ya buƙaci al’ummar yankin da su haɗa kai da hukumomin tsaro domin hana sake aukuwar irin wannan hari a nan gaba.
Zulum ya ce za a raba abinci da kayayyakin masarufi ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da magidanta da matan aure, tare da faɗaɗa tallafi ga al’ummomin da ke karɓar ’yan gudun hijira.
Ya ƙara da cewa za a ci gaba da tattaunawa da kwamandojin sojoji da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin.
“A yau za mu gana da jami’an tsaro domin duba hanyoyin inganta tsaro a wannan yanki,” in ji gwamnan.
Zulum ya bayyana cewa nasarar ayyukan tsaro na dogara ne da haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ƙungiyoyin sa-kai na yankin, ciki har da Sibilian JTF, mafarauta da ’yan banga.
Gwamnan ya samu rakiyar Sanata Mohammed Ali Ndume da sauran jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Gwoza.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link