Harin asibiti ya yi ajalin mutum 64 a Sudan — WHO

[ad_1]



Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce aƙalla mutum 64 ne suka mutu, ciki har da ƙananan yara 13, sakamakon wani hari ta sama da aka kai Asibitin Koyarwa na El-Daein da ke yankin Darfur a Sudan.

Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa harin ya kuma yi sanadiyar jikkatar mutum 89, ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya takwas, tare da kashe ma’aikatan jinya mata biyu da likita ɗaya.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Ghebreyesus ya ce harin ya lalata asibitin gaba ɗaya, lamarin da ya sa ba zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa ba, wanda hakan zai ƙara jefa al’ummar yankin cikin matsanancin hali na rashin kulawar lafiya.

Ya ƙara da cewa, hare-haren da ake kai wa cibiyoyin kiwon lafiya a Sudan sun haura 2,000, lamarin da ke ƙara ta’azzara matsalar jin ƙai da ake fuskanta a ƙasar.

Shugaban na WHO ya yi gargaɗin cewa hare-haren kan asibitoci da ma’aikatan lafiya na da mummunan tasiri nan take da kuma na dogon lokaci, musamman ga al’ummomin da sun daɗe suna fama da ƙarancin kayan kiwon lafiya da agajin gaggawa.

“An zub da jini fiye da ƙima, an jikkata jama’a. Lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen rikicin Sudan tare da kare rayukan fararen hula da ma’aikatan lafiya,” in ji shi.

Ya jaddada cewa bai kamata a riƙa kai hari kan cibiyoyin kiwon lafiya ba, yana mai cewa zaman lafiya ne mafita mafi dacewa ga rikicin da ke ci gaba da addabar ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *