Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe

[ad_1]



Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da fitar da Naira biliyan 5.8 domin biyan haƙƙin tsoffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.

Kwamishinan kuɗi na jihar, Mohammed Abatcha Geidam, ya ce wannan mataki na nuna yadda gwamnatin ke ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikatanta, musamman waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Ya ce gwamnan ya bayar da umarni cewa daga yanzu, biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata zai zama cikin jadawalin kuɗin wata-wata kamar yadda ake biyan fansho.

“Ina nufin daga yanzu za a riƙa biyan kudin a kowane wata tare da fansho, domin kauce wa taruwar bashi kamar yadda ya taɓa faruwa a baya,” in ji Kwamishinan.

Geidam, ya ƙara da cewa amincewar gwamnan babban mataki ne na tabbatar da cewa duk wani ma’aikaci da ya yi ritaya zai samu haƙƙinsa yadda ya dace.

“Hakan zai dawo da mutuncin tsoffin ma’aikata kuma ya tabbatar da cewa gwamnati tana nuna kulawa ga waɗanda suka yi mata hidima da gaskiya,” in ji shi.

Kwamishinan, ya bayyana cewa ma’aikatar kuɗi da ofishin shugaban ma’aikata suna aiki tare domin tabbatar da cewa an biya waɗanda abin ya shafa cikin lokaci ba tare da wata matsala ba.

Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na tsarin tattalin arziki da zamantakewa na Gwamna Buni domin tabbatar da jin daɗin al’ummar Jihar Yobe, musamman tsoffin ma’aikata da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *