Ban Ce Ba Zan Shiga APC Ba, Amma Dole A Kafa Sharuɗɗa – Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce baiƙi amincewa da ƙudirin ya sauya sheƙa zuwa APC ba amma ya dage cewa, dole a bayyana kuma a bayar da tabbaci a fili game da makomar Gwamnatin Jihar Kano da kuma jin daɗin magoya bayansa.
Kwankwaso ya bayyana wannan matsayin nasa ne a ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road a Kano yayin da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya da magoya baya daga Kananan Hukumomin Rano da Dawakin Tofa, da kuma sauran mambobin Ƙungiyar Kwankwasiyya.
- An Gabatar Da Sanarwar Taro Na 5 Na Hukumar Koli Mai Sa Ido Kan Tabbatar Da Da’a Ta JKS Karo Na 20
- ‘Yan Majalisar PDP Sun Yi Allah-wadai Da Zargin Alaƙanta Gwamnan Bauchi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci
“Ban ce ba zan shiga APC ba, amma dole ne mu fara tabbatar da makomar gwamnatin Jihar Kano kafin mu shiga APC. Menene makomar ‘yan majalisarmu da sauran magoya bayanmu kafin mu yarda mu fice?” in ji shi.
Tsohon gwamnan ya tuna da abubuwan da suka faru a baya na siyasa inda ƙungiyarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnatoci amma daga baya aka mayar da su saniyar ware.
“A baya, mun shiga kuma mun ba da gudummawa wajen kafa gwamnati, amma daga baya aka yi watsi da mu. Shi ya sa muka bar jam’iyyar. Shin yanzu sun canza matsayinsu game da mu? Kowa ya san rawar da muka taka a wancan lokacin,” in ji shi.