Likitoci sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki

[ad_1]



Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya sabon wa’adin kwana ɗaya domin ta cika buƙatun da take nema.

Hakan dai na zuwa ne bayan wa’adin farko na kwanaki 10 da suka bayar, wanda ya ƙare a ranar Talata, 10 ga Satumba.

Matakin da ƙungiyar ta ɗauka na zuwa ne a ƙarshen wani taron gaggawa da shugabanninta suka gudanar a ranar Laraba, domin nazarin ci gaban da aka samu tun bayan bayar da wa’adin farko.

Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a gagauta aiwatar da matakan da aka yi masu alƙawari.

Tun dai cikin wata sanarwa da ƙungiyar likitocin ta fitar a ranar 1 ga Satumba, 2025, ta buƙaci a biya mambobinta bashin ƙarin albashin watanni biyar da suka biyo, bayan aiwatar da ƙarin albashi tsakanin kashi 25 zuwa 35 cikin 100 da aka amince wa ma’aikatan lafiya.

Haka kuma, likitocin sun gabatar da wasu buƙatun da suka haɗa da gagauta biyan su bashin alawus-alawus ɗinsu da kuma sauran buƙatu da suka shafi jin daɗin aiki da walwala.

Likitoci masu neman ƙwarewar aiki a Najeriya su ne ƙashin bayan aikin kiwon lafiya a ƙasar, inda suke gudanar da ayyuka asibitoci mallakin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.

Duk lokacin da suka shiga yajin aiki ana samun koma baya wajen kiwon laiyar al’umma, lamarin da ke jefa rayuwar marasa lafiya ciki halin rashin tabbas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *