Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a Kano
[ad_1]
Don tunkarar zaɓen 2027, wata Ƙungiya a ƙarƙashin inuwar Tinubu/Barau/Atah Movement a ranar Alhamis a Kano ta shirya taron addu’o’i na musamman domin samun nasara ga shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin.
Taron addu’ar wanda ya samu halartar Malaman addinin Musulunci da magoya bayan jam’iyyar APC daga Ƙananan hukumomin Jihar 44, an gudanar da shi ne a Gidan Baballiya Kurna da ke Ƙaramar hukumar Fagge.
A yayin taron addu’o’in malaman sun kammala karatun Alkur’ani mai girma tare da gabatar da addu’o’i na musamman kan takarar Tinubu a wa’adi na biyu da kuma burin Barau ya zama Gwamna a 2027.
Malaman sun kuma yi addu’ar Allah Ya ƙara wa ƙasar nan zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki, ci gaban ƙasa da kwanciyar hankali a siyasance.
Da yake zantawa da manema labarai, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya taron, Seyi Olorunshaya, ya ce an gudanar da taron ne domin marawa Tinubu baya da kuma yunƙurin Sanata Barau Jibrin na zama Gwamnan Jihar Kano.
“Shugaba Tinubu ya yi ƙoƙari cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa, dubi ayyukan hanyoyi, farashin abinci da ke ci gaba da faɗuwa, samar da ayyukan yi da kuma ƙoƙarinsa kan tsaro,” in ji Olorunshaya.
“A cikin ’yan shekarun da suka gabata, ’yan Najeriya da a baya suka yi ta kuka a kullum kan rashin tsaro, tsadar kayayyaki da sauran kayayyaki, yanzu sun fara ganin sauyi na gaske tare da alamun samun mafita mai kyau.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link