Gwamnati ta wajabta miƙa ‘Project’ kafin zuwa NYSC

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC).

Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar.

Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka yi karatu.

Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD).

Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba.

Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi da bincike a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *