Za a biya tsofaffin ma’aikatan ƙananan hukumomi kuɗaɗe a Yobe
[ad_1]
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da fitar da Naira biliyan 2.1 cikin gaggawa domin biyan wasu maƙudan kuɗaɗe ga tsofaffin ma’aikatan ƙananan hukumomin da suka yi ritaya daga watan Janairu 2020 zuwa Mayu 2025.
Amincewar wanda Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da masarautu, Ibrahim Adamu Jajere ya sanar ya ƙara jaddada aniyar gwamnatin Buni na girmama tsofaffin ma’aikatan bisa ga hidima da sadaukarwar da suka yi wajen ci gaban jihar.
A cewar Kwamishinan, umarnin na Gwamna Buni ya kuma haɗa da kuɗaɗen garatuti cikin jadawalin kuɗaɗen ƙananan hukumomi na wata-wata, matakin da aka tsara don tabbatar da cewa waɗanda suka yi ritaya a nan gaba za su samu alawus na kuɗaɗen su cikin gaggawa ba tare da tara basussuka ba.
Jajere ya ce “Wannan wata alama ce ta nuna jin ƙai da jagorancin nagari na Gwamna Buni da nufin samar da agajin kuɗi da kuma dawo da martabar tsofaffin ma’aikatan mu don su samu rayuwa mai inganci su da iyalansu”.
Ya bayyana cewa tuni ma’aikatar ta fara shirye-shirye na gaskiya domin gaggauta raba kuɗaɗen da aka amince da su ga duk waɗanda suka cancanta a faɗin ƙananan hukumomin 17 da ke Jihar.
A cewarsa ware Naira biliyan 2.1 a matsayin kuɗaɗen tsoffin ma’aikatan ya kasance wani ɓangare na babbar ajandar sake fasalin Gwamna Buni don inganta kasafin kuɗi, adalci na zamantakewa da ingantacciyar rayuwa ga jama’ar Yobe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link