Kotu ta yi watsi da buƙatar sauya wa Kanu gidan yari
[ad_1]
Kotun Ƙolin Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da shugaban ƙungiyar yan awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya shigar na neman a sauya masa gidan yari daga Sakkwato
A zaman kotu da aka gudanar a ranar Talata, Mai Shari’a Omotosho ya ce tun a ranar 8 ga Disamba ya umurci Kanu da ya sanar da dukkan ɓangarorin da shari’ar ta shafa, wato Gwamnatin Tarayya da Hukumar Gyaran Hali, game da wannan buƙata.
Alƙalin ya ce, “Na umurce ka da ka tabbatar an sanar da waɗanda shari’ar ta shafa, amma babu wata hujja da ke nuna cewa an aiwatar da wannan umarni ko an sanar da su yadda ya kamata.”
Dangane da wannan hujjar ce, alƙalin ya ce buƙatar Kanu ba ta cika ka’idojin doka ba, saboda haka haka kotu ta yi watsi da ita.
A yayin zaman kotun, lauyan da ke kare Kanu, Demdoo Asan, ya shaida wa kotu cewa yana neman janye wa daga shari’ar, yana mai bayyana cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da wanda yake karewa da ba za a iya daidaitawa ba.
Ya ce Kanu na ƙoƙarin tsara abin da lauyansa zai faɗa a gaban kotu, al’amarin da ya ce a matsayinsa na jami’in kotu ba zai iya amincewa da shi ba.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Omotosho ya amince da buƙatar lauyan na janyewa daga shari’ar, inda ya yaba masa bisa yadda ya kiyaye martabar kotu da mutuncin aikin lauya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link