Ɓarawo Ya Sace Motar Masarautar Bauchi
[ad_1]
Wani ɓarawo ya fuskanci koma baya a ƙoƙarinsa na sace mota ƙirar Toyota Hilux mallakin Masarautar Bauchi.
Lamarin a faru ne a ranar 5 ga watan Janairu, yayin da wanda ake zargi da sace motar ya yi awun gaba da ita a lokacin da direban motar ya tsaya Domin yin fitsari a wani gidan mai.
- Harin Venezuela Ta’asa Ce Da Amurka Ke Tafkawa Tun Bayan Yakin Duniya Na Biyu
- Sojoji Sun Daƙile Harin Fashi Da Makami A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
Wani mai suna Buhari Musa Umar, daga masarautar Bauchi ya ankarar da ‘yansandan da ke sintiri a kan shataletalen hanyar Jos da ke Bauchi dangane da sace motar.
Musa ya yi bayanin cewa direban motar ya tsaya a gidan Man Inkiya da nufin kara mai ne a motar.
Direban motar ya yi bayanin cewa, yana kan hanyarsa ne ta zuwa Ganjuwa domin kai wani saƙon da Sarki ya aikesa.
Direban, bayan ya sha mai ya shiga bayan gida domin ya yi fitsari inda ɓarawon ya yi amfani da wannan damar wajen sace motar tare da arcewa da ita.
A sanarwar manema labarai a ranar Talata, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya ce, bayan samun labarin faruwar lamarin cikin gaggawa jami’ansu suka kai ɗauki domin nemo motar.
Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron sun samu nasarar kamo motar a layin Bayan Gari tare da cafke wanda ake zargin da sace motar.
SP Habib ya ƙara da cewa, a lokacin da ake yi wa wanda ake zargi da sace motar tambayoyi, ya amsa laifin da ake zarginsa da bakinsa.
Jami’in watsa labaran ya ƙara da cewa a kan ci gaba da gudanar da bincike, kuma da zarar aka kammala za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu domin ya fuskanci Shari’a daidai da laifinsa.
Har-ila-yau, Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya nanata aniyar hukumar na yin aiki tuƙuro domin kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.
A wani faifayin bidiyo an gano yadda jama’a suke ta bin ɓarawon da gudu a lokacin da ya ja motar da nufin tserewa da ita inda suka yi ta masa ihun ɓarawo ɓarawo, yayin da shi kuma ya yi ta jan motar da gudun tsiya da nufin arcewa.
[ad_2]
Source link