EFCC ta ƙwace kadarorin Malami na Naira biliyan 213
[ad_1]
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta samu sahalewar kotu na ƙwace kadarori na wucin-gadi da darajarsu ta kai Naira biliyan 213.2, waɗanda ake alaƙantawa da tsohon Ministan Shari’a kuma Tsohon Babban Lauyan Ƙasa, Abubakar Malami.
Wata Babbar Kotun Tarayya ce ta yanke hukuncin a ranar Laraba, inda bayanai ke nuna cewa wasu daga cikin kadarorin ana alaƙanta su da ’ya’yansa biyu, Abdulaziz Malami da Abiru-Rahman Malami, da kuma matarsa Asabe Bashir waɗanda ake zargin an mallake su ta hanyar da ba ta dace ba.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin, bayan lauyan Hukumar EFCC, Ekele Iheanacho SAN ya buƙaci hakan.
Cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an ƙiyasta darajar kadarorin waɗanda adadinsu ya kai 57 za ta kai naira N213,234,120,000 da ya mallaka a jihohin Kebbi da Kano da Kaduna da Abuja.
Haka kuma, Mai Shari’a Nwite ya umarci a buga sanarwar ƙwace kadarorin a wata jarida ta ƙasa, domin bai wa duk wanda ke da’awar wani haƙƙi a kansu damar bayyana kansa cikin kwanaki 14, tare da bayyana dalilin da ya sa ba za a mayar da kadarorin hannun gwamnatin tarayya ba kai tsaye.
A ƙarshe alƙalin ya ɗage shari’ar zuwa ranar 27 ga Janairu domin ci gaba sauraron ƙorafe-ƙorafen masu ruwa da tsaki.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 12 bayan da kotun ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’ar da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 kowannensu da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
A cewar kotun, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.
A watan Disambar da ya gabata ne ne dai Hukumar EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link