Shugaban Mali Ya Jaddada Matsayar Kasarsa Na Nacewa Manufar Sin Daya Tak A Duniya

[ad_1]

Shugaban kasar Mali Assimi Goita, ya ce kasarsa za ta ci gaba da nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya. Goita ya bayyana hakan ne a jiya Talata a birnin Bamako, yayin da yake karbar takardun kama aiki na sabon jakadan Sin a Mali mista Li Xiang.

Shugaban na Mali, ya kara da cewa kasarsa da Sin suna martaba akidu iri daya, suna kuma kan matsaya guda dangane da wasu muhimman batutuwa, kamar martaba ikon mulkin kai da tsare martabar yankuna, da adawa da tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe na daban, da amfani da wasu batutuwa, ko siyasantar da batun kare hakkin bil’adama. Ya ce Mali za ta ci gaba da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Shugaba Goita, ya ce kasarsa a shirye take ta yi aiki da Sin wajen aiwatar da muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ma sakamakon dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a birnin Beijing. Kana za ta ingiza aiwatar da karin muhimmman ayyuka dake kunshe cikin tsarin hadin gwiwar Sin da Mali, da tabbatar da al’ummun kasashen biyu sun ci gajiyar hakan.

A nasa bangaren kuwa, Li ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Mali, wajen aiwatar da muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da karfafa hadin gwiwa na zahiri, da fadada musaya tsakanin al’ummun sassan biyu, da bude sabon babin kawance tsakanin Sin da Mali a tafarkin gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya domin sabon zamani. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *