An yi wa Khamenei salatul ga’ib a Kano

[ad_1]



Gomman mabiya ɗarikar Qadiriyya sun gudanar da sallar jana’iza ta ga’iba (Salatul Ghaib) ga marigayi jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Aminiya ta ruwaito cewa, jana’izar wadda aka yi a ranar Litinin, ta gudana ne a Darul Qadiriyya da ke unguwar Kabara a cikin ƙwaryar birnin Kano.

Darul Qadiriyya shi ne gidan marigayi Sheikh Nasiru Kabara, jagoran ɗarikar Qadiriyya na Afirka, wanda ya rasu a shekarar 1993.

Babban ɗan marigayin, Sheikh Muazzamu Nasiru Kabara, ne ya jagoranci sallar, wadda aka gudanar nan take bayan sallar La’asar a harabar Darul Qadiriyya.

Mahalarta sallar waɗanda suka haɗa da fitattun malamai da mabiya ɗarikar, sun yi addu’o’i ga mamacin tare da roƙon Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba shi gidan Aljanna.

Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Sheikh Musal Qasiyuni Nasiru Kabara, wanda ke gabatar da karatun Kitab Al-Shifa duk rana tun farkon watan Ramadan a Darul Qadiriyya.

Sheikh Musal Qasiyuni Nasiru Kabara a wurin sallar

Malamin ya kuma wallafa bidiyon sallar a shafinsa na Facebook,wanda daman ya sanar da shirin gudanar da ita tun da fari.

An bayyana Khamenei a matsayin shahidi, bayan rahotannin cewa an kashe shi a wani hari da Amurka da Isra’ila suka kai Iran a ranar Asabar.

Salatul Ga’iba wata sallah ce ta jana’iza da ake yi wa mamaci ba tare da gawarsa tana nan ba, musamman idan ya rasu a wajen da babu Musulmi da za su yi masa jana’iza.

Annabi Muhammad (SAW) ne ya fara yin sallar ga’iba ga Sarkin Habasha mai suna Najashi lokacin da ya rasu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *