Zulum ya ƙaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta 300,000

[ad_1]



Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da tallafin rabon kayan abinci na Ramadan ga magidanta 300,000 a faɗin ƙananan hukumomi 27 da ke jihar.

Rabon abincin an ƙaddamar da shi ne a filin wasa na Ramat Square da ke babban birnin jihar Maiduguri, an tsara shi ne don rage wahalhalun tattalin arziki da mazauna karkara ke fuskanta a lokacin watan Ramadan mai alfarma.

A ƙarƙashin shirin, kowane magidanci mai cin gajiyar zai sami buhun shinkafa ɗaya, buhun gero ɗaya da kuma kilo 10 na sukari – muhimmancin rabon kayan abincin nada nufin rage wa iyalan da ke fama da hauhawar farashin kaya.

A jawabin da ya yi wa taron masu cin gajiyar da shugabannin al’umma, Zulum ya yi gargaɗi mai tsauri game da karkatar da kayan agajin.

Wakilinmu ya tuntuɓi Dauda Iliya mai taimakawa Gwamna Zulum kan harkokin manema labarai ya tabbatar da wannan adadi na magidanta 300,000 da za su ci gajiyar kayan tallafin a Ramadan

“Ga kwamitin da ke kula da wannan rabon, gaskiya ta zama abin lura a gare ku. Adalci ya zama jagorar ku,” in ji Gwamnan.

Ku sani waɗannan kayayyaki ba na sayarwa ba ne, ba na abokanka ko ‘yan uwanka ba ne na waɗanda suka cancanta da a ba su ne da ke cikin al’umma.

“A cikin su akwai gwauraye, marayu, ‘yan gudun hijira, manomi wanda gonakinsa ba su gama murmurewa ba, da kuma mai karɓar albashi na yau da kullun da ke fama da wahalar biyan buƙatun rayuwa.”

“Don haka duk wani jami’i da aka samu yana karkatar da waɗannan kayayyaki ga buƙatunsa zai fuskanci fushin doka.”

Gwamnan ya kuma umarci al’ummomin da ke gudanar da azumin Ramadan na wannan shekarar da su amfana da wannan kyautar, yana mai jaddada tsarin gwamnatinsa na haɗa kan jama’a.

“Wannan tallafin za ta kuma shafi hatta waɗanda ba Musulmi ba waɗanda ke azumin dai-dai da wanda ya faɗo a cikin watan Ramadan,” in ji Zulum.

Wannan matakin ya kara ƙarfafa abin da masu lura suka bayyana a matsayin tsarin tallafawa addinai daban-daban a ƙarƙashin jagorancin Zulum.

A kowace shekara, gwamnan yana amincewa da rarraba abinci ga Kiristoci masu aminci a lokacin Kirsimeti kuma yana ba da sufuri kyauta ga Kiristocin da ba ‘yan asalin jihar ba da ke son tafiya gida don bukukuwan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *