Me Ya Sa Karin Kasashen Duniya Ke Yin Na’am Da Bikin Bazara?


A kwanakin nan, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da shagalin murnar bikin bazara, wato bikin sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa, don isar da fatan alheri ga Sinawa da ma aminan kasa da kasa, wanda kuma ya nuna wa duniya al’adu nagari na kasar Sin.

Kasancewarsa bikin gargajiya mafi muhimmanci ga al’ummar kasar Sin, karin kasashen duniya na yin na’am da bikin bazara, musamman sabo da irin ma’anar da bikin ya kunsa. Kafin bikin, shugabannin kasashe da na kungiyoyin duniya da dama ne suka mika sakwanninsu na fatan alheri game da bikin. A sa’i daya kuma, an shirya shagulgula masu kayatarwa a kasashe da dama, don murnar bikin da kuma rungumar al’adun kasar Sin.

A yayin da ake fuskantar tashin hankali a duniya, yadda kasar Sin ke ta inganta bunkasarta da dada bude kofarta ga ketare, ya samar da tabbas da ake matukar bukata a duniya, abin da ya sa kasa da kasa suka yi na’am da ita. Don haka, al’ummar kasa da kasa na kara fatan samun fahimtar kasar Sin, dalilin da ya sa al’adun kasar Sin ke kara samun karbuwa a kasa da kasa.

A yayin da ake murnar bikin bazara, irin ra’ayoyi da al’adun gargajiyar kasar Sin suka kunsa na kasancewar mabambantan al’adu tare duk da bambancinsu, da yin musaya a tsakaninsu, yana samun karin amincewa daga kasashen duniya. Da fatan al’ummun duniya za su hada hannu da juna, su kara fahimtar juna, don kawar da bahaguwar fahimta da rikici a tsakaninsu, da kuma rungumar kyakkyawar makomarsu.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *