An Fitar Da Sakon Bidiyo Na Yayata Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Tunisia

[ad_1]

An gudanar da wasan kwaikwayo mai jigon “Bikin bazara mai dadi da hanyar siliki mai kyau” na 2026 a cibiyar al’adu dake Tunis, babban birnin kasar Tunisia daga ranar 31 ga Janairu zuwa 1 ga Fabrairu bisa agogon wurin, inda aka fitar da sakon bidiyo na yayata shirye-shiryen bikin bazara na shekarar Doki na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a takaice.

Ministan waje da ministan al’adu na Tunisia, da jakadun Sin da na saruran kasahe dake Tunisia, da shugabannin hukumomin da suka shafi al’adu na Tunisia da sauran baki sama da 300 sun halarci bikin, kana kusan masu kallo 1500 na Tunisia sun kalli wasannin.

Bugu da kari, a ranar 1 ga watan Fabrairu, an gudanar da bikin murnar bikin bazara a kwalejin Confucius ta jami’ar Yerima Sultan ta Saudiya. A yayin bikin, an nuna sakon bidiyo na yayata shirye-shiryen bikin bazara na CMG da aka yi da harsunan Turanci da Larabci, wadanda suka jawo hankulan adadi mai yawa na malamai da dalibai na Sin da Saudiya. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *