NDLEA Na Neman Al’umma Ta Goyi Bayan Shirye-shiryenta Na Yaƙi Da Noman Wiwi
[ad_1]
Shugaban Hukumar Yaki da Ta’ammuli da Miyagun Kwayoyi ta Lasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Marwa (mai ritaya), ya yi kira da a goyawa hukumar baya kan sabbin shirye-shiryen da ta samar kwanan nan game da dakile yaduwar haramtattun ƙwayoyi a kasar.
Shirin, wanda aka tanada da nufin hana shan wiwi a Afirka, don dakile noman wiwi ba bisa ka’ida ba, wanda shirin kuma zai habaka al’ummomin karkara da kuma karfafa tsaron kasa.
- Kashi 72 Na Ɗalibai Sun Lashe Jarabawar NECO Ta 2025
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama A Sansanin Gwaska Ɗanƙarmi A Jihar Zamfara
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata don wayar da kan al’umma da nufin samun goyon bayansu ga shirin, wanda aka kaddamar a matsayin shirin gwaji a cikin al’ummomi uku da ke noman wiwi a jihar Ondo a makon da ya gabata, Marwa ya ce manufar ta zarce maye ribar noman wiwin, yana mai jaddada cewa “fa’idodinta sun hada da: karfafa tattalin arzikin karkara ta hanyar bunkasa darajar kayayyaki; rage nauyin da ke kan jami’an tsaro da na cibiyoyin tsarin shari’a”;
Har ila yau, “shirin zai inganta zaman lafiya da hadin kan zamantakewa a yankunan da a ke fama da yawaitar aikata laifuka. Shirin zai inganta matsayin Nijeriya a duniya a fannin kula da haramtattun kwayoyi da hadin gwiwar ci gaba a duniya.”
Ya kuma yi kira ga al’ummomi a faɗin ƙasar, musamman waɗanda suka fuskanci matsalar noman wiwi ba bisa ƙa’ida ba, da su rungumi tsarin kuma su yi aiki tare da NDLEA wajen gina hanyoyin rayuwa na halal, masu amfani, da aminci.
[ad_2]
Source link