Jirgi Marar Matuki Mai Dakon Kaya Irinsa Na Farko A Duniya Ya Yi Tashinsa Na Farko Cikin Nasara
[ad_1]
Jirgi marar matuki mai dakon kaya samfurin CH-YH 1000s ya yi tashinsa na farko cikin nasara a ranar 1 ga watan nan. Kamfanin nazarin fasahohin sararin samaniya na kasar Sin (CASC) ne ya kirkiro jirgin, kuma jirgin yana amfani da mai da kuma lantarki, wanda ya kasance irinsa na farko a duniya.
An inganta jirgin ne daga asalin samfurin jirgi na CH-YH 1000, kuma ta hanyar hadin gwiwa da kamfanonin kera motocin lantarki da ke sahun gaba, an inganta karfin jirgin, matakin da ya yi matukar rage tsawon hanyar da yake bukatar gudu kafin ya tashi ko sauka, tare da kara nauyin kayayyakin da yake iya dauka da kuma tsawon hanyar da yake iya tafiya. Wannan ya kuma kasance karo na farko da aka hada muhimman fasahohin kera jiragen sama marasa matuki da motoci na kasar Sin, da ma tsarukan samar da su, kuma ta hakan aka yi matukar rage kudin samar da jirgin .
Za a iya yin amfani da jirgin samfurin CH-YH 1000s ta fannin jigilar kayayyaki da samar da agajin gaggawa da sauya yanayi bisa bukatun dan Adam da sa-ido a kan teku da sauransu. (Lubabatu Lei)
[ad_2]
Source link