‘Muna kiran likitoci ’yan Kano da ke aiki a jihohi maƙwabta da su dawo gida’

[ad_1]



Gwamnatin Kano ta sanar da cewa ta tanadi aiki kai tsaye ga duk wasu likitoci ’yan asalin jihar da ke aiki a wasu jihohi maƙwabta, a wani mataki na ƙara ƙarfafa harkokin kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da ke faɗin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da wannan amincewar, kamar yadda wata sanarwa da Hukumar Kula da Asibitocin Kano ta fitar ta bayyana.

Sanarwar ta ce gwamnatin tana kira ga duk likitocin ’yan Kano da ke aiki a waje da su dawo gida domin karɓar aiki a asibitocin jihar, da zummar cike giɓin ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyuka a fannin kiwon lafiya.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta aiwatar da cikakken tsarin albashin likitoci na CONMESS, daidai da tsarin da gwamnatin tarayya ta amince da shi, tare da tabbatar da cewa duk likitan da ya dawo Kano zai ci gaba da riƙe matsayin da ya kai a wurin aikin da ya fito.

Baya ga albashi, gwamnatin jihar za ta ba likitocin damar cin gajiyar Asusun Horar da Likitocin Kwarewa (Medical Residency Training Fund – MRTF), da kuma damar samun horon ƙwarewa na residency a cikin gida a wasu fannoni na musamman.

Fannonin da za a horar da likitocin sun haɗa da Cututtukan Ciki, Kiwon Lafiyar Iyali, Cututtukan Kunne, Hanci da Maƙogwaro (ENT), da kuma Kiwon Lafiyar Mata da Haihuwa, tare da alƙawarin ƙarin tallafi da sauƙaƙe yanayin aiki nan gaba.

An umurci dukkan likitocin da suka cancanta da su garzaya nan take zuwa hedikwatar Hukumar Kula da Asibitocin Kano domin tantancewa, cike takardu da kuma ɗaukar su aiki a hukumance.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Hukumar, Dokta Mansur Mudi Nagoda, ta ce wannan shiri na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin magance ƙarancin ma’aikatan lafiya da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin Jihar Kano.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *