Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki
[ad_1]
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 don ɗaukar mataki game da buƙatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aiki.
Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki 10 da suka bayar a baya.
Tuni wasu likitoci a Abuja da Jihar Oyo suka tsunduma yajin aiki.
Likitocin, waɗanda yawancinsu ke aiki a Asibitocin Koyarwa da na Ƙwararru, suna yawan tafiya yajin aiki saboda rashin biyan wasu haƙƙoƙinsu.
A halin yanzu, suna neman a biya su kuɗin horon 2025 da bashin albashin da suka bi, sannan sun buƙaci a hanzarta biyansu wani kuɗaɗen alawus-alawus.
Hakazalika, sun buƙaci gwamnati ta amince da takardar shaidar digiri ta ‘West African postgraduate’, sannan a magance matsalolin da suka shafi walwalarsu a Jihar Kaduna da kuma Asibitin Koyarwa na LAUTECH, da ke Ogbomoso.
Shugaban NARD, Dokta Tope Osundara, ya ce wannan mataki da suka ɗauka ya biyo bayan taron awanni shida na kwamitin gudanarwa na ƙasa da suka gudanar ta Intanet.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta yi alƙawarin ɗaukar mataki game da buƙatunsu amma dole ne a hanzarta aiwatar da su.
Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta yi wani abu a kan buƙatun nasu ba, za su fara yajin aiki a ranar Juma’a.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link