2026: Akpabio Ya Janye Dukkan Ƙararrakin Ɓatanci Bayan Shan Ruwan Wa’azi
[ad_1]
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya umarci lauyoyinsa da su janye duk wata ƙara da ya shigar kan mutane da dama, yana mai cewa, wa’azin malaminsa na coci da ya saurara kan ibadar sabuwar shekara, ya taɓa masa zuciya.
Da yake jawabi a Sacred Heart Parish da ke Uyo a ranar Alhamis, Akpabio ya ce ya shigar da kararraki kusan tara kan wasu mutane da yake zargin su da ɓata masa suna.
- Gwamnan Filato Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
- Da Ɗumi-Ɗumi: Chelsea Ta Raba Gari Da Koci Enzo Maresca
Ya ce, “Na shigar da ƙararraki kusan tara a kotu kan wasu mutane da suka ɓata min suna, suka yi min ƙarya.
“Amma na saurari wa’azin malamin majami’a kuma na fahimci da ni yake, don haka, ina umurtar lauyana da ya janye dukkan ƙararrakin da aka shigar kan waɗanda suka ɓata min suna.”
A shekarar 2025, Akpabio ya shigar da ƙararraki da dama kan zargin ɓata masa suna, ciki har da ɗaya kan abokiyar aikinsa, Sanata Natasha Akpoti‑Uduaghan.
A ƙarshen shekarar 2025, Akpabio ya shigar da ƙarar Natasha inda ya nemi ta biya shi zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 200 bisa zargin ƙaryar da yace ta yi masa na zargin neman lalata da ita, wanda ya musanta kuma ya bukaci ta tabbatar da zarginta a kotu.
[ad_2]
Source link