Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwaransa Na Koriya Ta Kudu Ta Wayar Tarho
Mamban hukumar siyasar kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS kuma ministan wajen kasar, Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Koriya ta Kudu, Cho Hyun ta wayar tarho jiya Laraba.
A zantawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, a karkashin jagoranci bisa tsare-tsare na shugabannin kasashen biyu, dangantakar Sin da Koriya ta Kudu ta sami farfadowa, kuma ta koma madaidaiciyar hanya, wanda ya nuna cewa dangantakar ta samu ci gaba mai kyau sannu a hankali. Sin na mai da hankali sosai tare da maraba da shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae-myung ya kawo ziyarar aiki a nan Sin, kuma ana fatan bisa kokarin da kasashen biyu suka yi, ziyarar za ta inganta dangantakar abokantaka bisa tsare-tsare tsakanin Sin da Koriya ta Kudu tare da samu sabbin ci gaba.
Wang Yi ya kara da cewa, shekarar 2025 shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar Sin a yaki da hare-haren sojojin Japan. Game da yunkurin wasu ’yan siyasa daga Japan na komawa ’yar gidan jiya, don soke hukuncin lafukan kai hare-hare da mulkin mallaka da kasar ta yi, an yi imanin cewa bangaren Koriya ta Kudu zai dauki nauyin isar da tarihi ga jama’a, kuma zai dauki matsayin da ya dace, da kiyaye adalcin kasa da kasa wanda ya hada da bin ka’idar kasar Sin daya tak a kan batun yankin Taiwan.
A nasa bangaren, Cho Hyun ya bayyana cewa, shugaba Lea Jae-myung na Koriya ta Kudu ya dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwa tare da Sin, ya tsaya tsayin daka wajen bunkasa dangantakar abokantaka bisa tsare-tsare tsakanin Sin da Koriya ta Kudu. Bangaren Koriya ta Kudu na fatan yin aiki tare da Sin, don tabbatar da ziyarar aikin shugaba Lea Jae-myung a Sin ya kammala lami lafiya. Kuma Koriya ta Kudu ba za ta canza matsayarta ta mutunta ka’idar kasar Sin daya tak a duniya ba. (Safiyah Ma)