Guterres Ya Zargi Amurka Da Take Dokar Ƙasa Da Ƙasa A Venezuela

[ad_1]

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana damuwa kan abin da ya kira karya dokokin ƙasa da ƙasa a Venezuela.

Ya faɗi haka ne cikin wani saƙo da aka karanta a taron gaggawa da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira domin tattauna halin da ake ciki a Venezuela, bayan zargin tsoma bakin Amurka a harkokin ƙasar.

  • Sakataren APC Ya Buƙaci Murabus Ɗin Wike Saboda “Tsoma Baki” A Harkokin Jam’iyya
  • AFCON 2025: Super Eagles Sun Murƙushe Mozambique Da Ci 4–0

Guterres ya ce rashin mutunta dokokin ƙasa da ƙasa na iya haddasa rikici da rashin zaman lafiya a Venezuela, tare da kawo matsala ga tsaron yankin baki ɗaya.

Ya kuma yi gargaɗin cewa hakan na iya lalata dangantaka tsakanin ƙasashe.

Sakataren ya buƙaci dukkanin ɓangarori su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, su kuma warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya, domin kauce wa rikici da ƙara taɓarɓarewar al’amura.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *