Yara 469 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Kano
[ad_1]
Aƙalla yara 469 ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, 2025, a Jihar Kano, yayin da kashi 51.9 cikin 100 na yara ke fama da rahsin na girma yadda ya kamata.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Farfesa Ruqayya Aliyu Yusuf na Sashen Nazarin Harkokin Watsa Labarai, Jami’ar Bayero Kano (BUK), a lokacin da take gabatar da takarda mai taken: “Understanding the Basics of Behavioural Change: Towards Improving Malnutrition in Kano State” a wani taron horaswa ga ’yan jarida.
Farfesa Ruqayya ta ce rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin kyawawan dabi’un cin abinci shi ne babban ƙalubale a Kano, duk da cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da aka fi haskawa a Global Nutrition Index.
Ta ce bisa rahoton UNICEF na 2025, kashi 40 cikin 100 na yara ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da nakasu na girma, yayin da a Kano kashi 51.9 cikin 100 ke fama da matsalar.
Farfesan ta nuna damuwa kan lamarin, inda ta ce, “Rashin abinci mai gina jiki na da alaƙa da talauci, rashin wadataccen abinci, dabi’ar cin abinci marasa kyau da kuma ƙarancin wayar da kan jama’a kan harkokin lafiya.”
A nata jawabin, Masanin Kimiyyar Amfanin Gona, Amina Ado Yahaya, ta bayyana cewa Kano ce ke da mafi yawan yara ƙasa da shekaru biyar da ke fama da rashin nauyi, da kashi 42.6 cikin 100, lamarin da ya kamata ya sa a ƙarfafa noman kayan lambu a gida domin inganta abinci mai gina jiki.
Ta kuma ce rashin sinadarin Vitamin A na daga cikin manyan dalilan makanta a yara, tare da ƙara tsananta cututtuka kamar shan inna da gudawa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link