NNPP Ta Buƙaci INEC Ta Yi Watsi Da Tarukan Jam’iyyar Da Kwankwaso Zai Jagoranta
[ad_1]
Jam’iyyar NNPP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ‘yan Nijeriya da su yi watsi da tarukan jam’iyya da ake ikirarin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso zai jagoranta, inda ta bayyana cewa tarukan sun sab awa doka.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Ogini Olaposi, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa kotu ta umurci NNPP ta gudanar da tarukanta na kasa kuma an kammala su.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa Kwankwaso ya aika da wasika ga INEC, yana sanar da hukumar game da shirin gudanar da sabbin tarukan jam’iyya NNPP, daga 25 ga Nuwamba, zuwa Janairu 2026.
Jam’iyyar ta bayyana cewa kungiyar Kwankwasiyya ba za ta iya gudanar da babban taron jam’iyya a madadinta ba, saboda yarjejeniyar da aka kulla zaben shugaban kasa na 2023 ya shude.
Jam’iyyar ta lura cewa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP na 2023, da wasu ‘yan kungiyar Kwankwasiya sun ci gaba da ficewa daga cikin jam’iyyar saboda cin amanan jam’iyyar.
“Har yanzu muna mamakin cewa wani mutum mai matsayi kamar na Kwankwaso zai nace wajen sace jam’iyyar da ta ba shi takara a zaben shugaban kasa na 2023 kyauta.”
NNPP ta bayyana cewa INEC dole ne ta cika nauyin da ke kansa ta hanyar bin dokokin kotu da kuma saka sahihan shugabannin jam’iyyar a adireshinta na intanet.
“Babbar kotun ta Jihar Abiya da babbar kotu a Abuja sun tabbatar da hana Kwankwaso da kungiyarsa daga shiga tsarin dimokuradiyya na cikin gida na NNPP kuma idan ya saba za a ladabtar da shi.
Abun bakin ciki ne cewa ana iya ganin Kwankwaso yana gudanar da kansa cikin rashin girmamawa ta hanyar kin bin hukuncin kotu da kuma karya doka.
“Shugabancin INEC na baya ya gaza mana, kuma muna fatan cewa shugabanci na yanzu zai nisanci rashin biyayya ga bin doka da oda na al’umma.
“Har yanzu muna mamakin dalilin da ya sa INEC ba ta mayar da martani ga wasikunmu da ke bukatar a mutunta bin hukuncin kotuna ba.
“A matsayinta na mai yanke hukunci, bai kata INEC ta ci gaba da zura ido kan al’amurar da ke bukatar hukunci cikin gaggawa ba da suka shafi zaman lafiyar al’umma.”
A cewar jam’iyyar, INEC tana da masaniya game da hukuncin kotu, duk da haka, tana mai da hankali ga kungiyoyin da ke son haddasa rikici a cikin dimokuracdiyyar Nijeriya.
“Mun rubuta wasiku da dama zuwa INEC kan wadannan lamarin, duk da haka, hukumar ta yi burus wanda hakn yana karfafa rashin biyayya ga dokokin Nijeriya.
“A karkashin irin wannan yanayi, za mu ci gaba da kiyaye zaman lafiya ga al’umma kuma mun umurci ‘yan jam’iyyarmu su yi watsi da taruka da zaben shugabannin jam’iyyar na bogi.
“Muna kara kira ga INEC ta taimaka wa dimokiradiyya tare da ceto Nijeriya. Ajandar sabon fata ta gwamnatin tarayya a yanzu za ta iya samun nasara ne kawai idan ana bin dokoki kuma ana girmama su”.
[ad_2]
Source link