ISWAP ta harbi Dagaci, ta sace direba a Yobe
[ad_1]
’Yan bindiga da ake zargin mayaƙan ISWAP ne sun raunata wani dagacin ƙauye, suka sace direba a Ƙaramar Hukumar Geidam a jihar Yobe.
An kai hare-haren ne da misalin ƙarfe 12:20 na rana a ranar 27 ga Disamba, 2025 inda suka harbi dagacin ƙauyen Ja Jibiri, Lawan Hassan, mai shekaru 45, a kafaɗarsa ta hagu.
Daga nan maharan suka tafi ƙauyen Ladu, inda suka yi garkuwa da wani direba mai shekaru 40, suka shiga cibiyar kula da lafiya a matakin farko, suka sace magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya masu daraja da wata mota ƙirar Volkswagen Golf.
Bayan ’yan ta’addan suka janye an garzaya da dagacin zuwa Babban Asibitin Geidam don kula da lafiyar sa.
Jami’an tsaro a yankin sun bayar da rahoton cewar, suna cikin shirin ko-ta-kwana, yayin da ake ci gaba da sa ido da ƙoƙarin gano waɗannan ’yan ta’addan.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link