’Yan bindiga sun kashe mutum 17, sun kone kasuwar kauye a Binuwai
[ad_1]
’Yan bindiga sun kashe mutum 17, ciki har da ɗan sandan kwantar da tarzoma, a harin da suka kai wata kasuwa da ke kauyen Abande a karamar hukumar Kwande ta jihar Bin.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa harin, wanda ya faru a ranar Talata, ya auku ne a ranar kasuwar kauyen, lokacin da jama’a ke tsaka da saye da sayarwa.
Wani tsohon Kansila a yankin, Akerigba Lawrence, ya ce maharan sun bude wuta kan ’yan kasuwa da mazauna yankin, inda suka kashe mutane da dama nan take.
Ya ce maharan sun kuma yi wa shaguna fashi, inda ’yan kasuwa suka yi ikirarin cewa kuɗi da kayayyaki da darajarsu ta haura Naira miliyan 150 aka kwashe kafin daga bisani a ƙone duk kasuwar.
Lawrence ya ce da misalin ƙarfe 11:55 na daren Talata, an kwashe gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe zuwa Jato-Aka ta hannun jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke yankin.
Ya lissafa sunayen waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu da suka haɗa da Iornunbe Agba, Chia Kile, Terseer Shenge, Mker Ugbe, Emmanuel Agba Ortswen, Gbinde, da kuma ɗan sandan wanda shi ne kwamandan rundunar da ke aiki a lokacin harin, da sauran mutane.
Tsohon jami’in ƙaramar hukuma ya kuma ce har yanzu ba a san inda wasu mazauna yankin suke ba a lokacin da ake hada wannan rahoto.
Lawrence ya ƙara da cewa wannan sabon hari ya ƙara tsoratar da mazauna Turan da makwabtan yankuna kan abin da ya bayyana a matsayin tabarbarewar tsaro a yankin.
Mutum 4 muka tabbatar an kasha – ’Yan sanda
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da mutuwar mutane huɗu a harin.
“Ranar 3 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, DPO na Jato-Aka ya samu kiran gaggawa cewa wasu da ake zargin makiyaya ‘yan bindiga, da yawa, sun kai hari kan jami’an ’yan sanda da ke yankin Abande da kuma al’ummar yankin.
“A yayin arangamar da ta biyo bayan martanin jami’an ’yan sanda, wani dan sanda mai mukamin ASP da ke aiki a Makurdi, wanda yake a kan aiki na musamman a yankin Abande, ya samu rauni mai tsanani har ya rasu.
“Abin takaici, mambobin al’umma huɗu ma sun rasa rayukansu sakamakon harin da ’yan bindigan suka kai.
“Bayan lamarin, an tura tawagar jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa yankin domin kare al’umma, gudanar da bincike, da kuma hana sake tabarbarewar tsaro. An kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa dakin ajiye gawa,” in ji ta.
Edet ta ƙara da cewa a martanin da aka yi kan harin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Benue, CP Ifeanyi Emenari, ya umarci Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Ayyuka da ya gaggauta zuwa yankin tare da kai ƙarin ’yan sanda da motocin domin jagorantar ayyukan tsaro, bin sawun maharan, da kuma kama su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link