Sin Ta Gudanar Da Atisayen Soja Mai Lakabin “Justice Mission 2025” A Yankin Rundunarta Dake Gabas
[ad_1]
Kakakin rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA yankin gabashi, kana babban kanar na sojan kasa Shi Yi, ya bayyana cewa, tun daga yau Litinin 29 ga watan Disamba, rundunar sojan PLA yankin gabashi, ta umurci sojojinta na kasa, da na ruwa da na sama, da sojojin roka da sauransu, da su shiga atisayen soja mai lakabin “Justice Mission 2025”, a mashigin tekun yankin Taiwan, da arewaci da kudu maso yammaci da kudu maso gabashi da kuma gabashin yankin na Taiwan.
A cewar kakakin, matakin zai fi mayar da hankali kan ayyukan sintiri na shirye-shiryen yaki ta ruwa da sama, da hadin gwiwar karbe iko bisa cikakken fifiko, da killace muhimman tashoshin jiragen ruwa da sararin teku dake yankin, da dakile hare-haren da kasashen waje za su iya kaiwa ta ruwan yankin Taiwan da sauransu.
Ban da wnanan kuma, za a bukaci jiragen ruwa da jiragen sama su kusanci tsibirin Taiwan ta hanyoyi daban-daban, kana sojoji nau’o’in daban daban su kai hare-hare tare, da nufin gwada kwarewar sojojin yankin a fannin hadin gwiwar yin yaki na gaske.
Shi Yi ya ce, matakin ya kasance babban gargadi ga ‘yan aware na yankin Taiwan, da sassan waje masu tsoma baki a harkokin yankin, kuma halastaccen aiki ne da ya wajiba don kare ikon mulkin kasa, da kuma tabbatar da dunkulewar kasa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link