Wang Yi Ya Gana Da Takwarorinsa Na Cambodia Da Thailand
[ad_1]
A jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasar Cambodia Prak Sokhonn da na kasar Thailand Sihasak Phuangketkeow, a birnin Yuxi na lardin Yunnan dake nan kasar Sin.
A yayin ganawarsa da Prak Sokhonn, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin na mayar da matukar hankali kan yanayin tashin hankali a yankin dake kan iyakar Cambodia da Thailand, tana kuma dukufa wajen dawo da bangarorin biyu kan teburin shawarwari domin shimfida zaman lafiya. Ya ce a yanzu haka, rundunonin sojan kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma kasar Sin ta taya bangarorin biyu murnar hakan. Kana, tana sa ran fitar da muryar lumana daga lardin Yunnan, domin cimma matsaya daya kan kiyaye zaman lafiya, tare da nuna makomar zaman lafiya.
A nasa bangare kuma, Prak Sokhonn ya ce Cambodia ta jinjinawa kasar Sin, game da aikin shiga tsakani da ta yi, tana kuma sa ran gaggauta shimfida zaman lafiya a yankin. Ya kuma yi fatan cewa, ganawar bangarori uku a wannan karo, za ta ba da gudummawar farfado da yanayin zaman lafiya na dindindin a yankin.
Bugu da kari, a yayin ganawarsa da Sihasak Phuangketkeow, Wang Yi ya ce, a matsayin amintacciyar makwabciyar kasar Thailand, kasar Sin ba ta son ganin barkewar rikici tsakanin Thailand da Cambodia. Ta kuma yi imanin cewa, idan kasashen biyu su yi shawarwari bisa adalci, da kuma hada kai wajen neman ci gaba, tabbas za su warware sabanin dake tsakaninsu lami lafiya.
A nasa bangare kuma, Sihasak Phuangketkeow bayyana fata ya yi cewa, Wang Yi zai mika sakon gaisuwar sarkin kasar Thailand Maha Vajiralongkorn ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, sa’an nan, ya ce, Thailand ta jinjinawa kasar Sin, game da shiga tsakani da ta yi domin shimfida zaman lafiya ta dabarar kasashen Asiya, kana Thailand za ta dukufa wajen cimma burin tsagaita bude wuta baki daya.
Bugu da kari, a yau Litinin ne aka gudanar da taron ganawar ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Cambodia da Thailand a birnin Yuxi, na lardin Yunnan na kasar Sin. Haka kuma, bayan ganawar, bangarorin uku sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana fannoni biyar, wadanda kasashen Cambodia da Thailand za su tabbatar da kara yin mu’amala da fahimtar juna, domin karfafa yanayin tsagaita bude wuta sannu a hankali, da farfado da mu’amalar dake tsakaninsu, da gina fahimtar siyasa, da kyautata dangantakar dake tsakaninsu, da kuma kare zaman lafiyar yankinsu baki daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link