AFCON 2025: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Karawar Nijeriya Da Morocco

[ad_1]

A yau Laraba, 14 ga watan Janairu, 2026, ƙasashen Nijeriya da Morocco za su fafata a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON 2025) da ake bugawa a ƙasar Morocco.

Za a buga wasan da misalin ƙarfe 9:00 na dare agogon Nijeriya, a filin wasa na Moulay Abdellah da ke birnin Rabat.

  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 32, Sun Kashe Mutum 1 A Kaduna
  • Sahihancin Sin Shi Ne Tubalin Hadin Gwiwarta Da Kasashen Afrika

Nijeriya ta kai wannan mataki ne bayan ta doke Algeria da ci 2–0 a wasan da ya gabata.

Ita ma Morocco ta samu nasarar doke Kamaru da ci 2–0.

A gasar ta bana, Nijeriya ta buga wasanni 5 ba tare da rashin nasara ba, yayin da Morocco ta ci wasanni 4 ta kuma yi canjaras ɗaya da Mali.

A tarihin haɗuwarsu, Nijeriya da Morocco sun haɗu sau 10.

Sun buga wasanni 5 a AFCON, 2 a gasar ‘yan wasan cikin gida (CHAN), sannan 3 a wasan sada zumunta.

Wasan da za a buga yau shi ne na 11 tsakaninsu.

Daga cikin wasanni 10 da suka gabata, Morocco ta fi samun nasara, inda ta doke Nijeriya sau 5, aka yi canjaras 1, yayin da Nijeriya ta doke Morocco sau 4.

Duk da haka, Nijeriya ta taɓa doke Morocco a irin wannan mataki na kusa da na ƙarshe a shekarar 1980, kuma a waccan shekarar Nijeriya ce ta lashe kofin bayan ta doke Algeria da ci 3–0 a wasan ƙarshe.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *