’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun yi garkuwa da gommai a Zamfara
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Dangoro da ke yankin Nahuche a ƙaramar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum uku, suka jikkata wasu, tare da yin garkuwa da adadin mutane da har yanzu ba a tantance ba.
Harin, wanda ya faru da tsakar daren Lahadi, ya kuma janyo ƙone gidaje da rumbunan ajiyar abinci, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya bayyana cewa ‘yan bindigar da ke dauke da makamai sun mamaye ƙauyen suka riƙa harbe-harbe sannan suka banka wa gidaje wuta.
Ya ce jami’an tsaro tare da ‘yan sa-kai sun kai ɗauki wurin da gaggawa, inda suka fafata da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa da raunukan harbi.
A cewarsa, mutum uku ne suka rasa rayukansu ciki har da wani jami’in tsaron al’umma, yayin da mutum biyar suka samu raunukan harbin bindiga, sai kuma wasu huɗu da suka samu ƙonuwa.
An kai dukkan waɗanda suka jikkata zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gusau domin samun kulawa, kuma ana sa ran za su farfaɗo.
Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane da dama, galibinsu mata, waɗanda har yanzu ba a san adadinsu ba.
Ya ƙara da cewa mazauna yankin da dama sun tsere zuwa garin Nahuche domin tsira da rayukansu, inda ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu agaji, ganin cewa maharan sun yi barazanar sake dawowa.
Rundunar ‘yan sanda ta ce tana ci gaba da farautar maharan, tare da jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin magance matsalar tsaro a jihar, bayan sauye-sauyen siyasa da suka gudana a kwanakin baya.

Masu alaƙa
[ad_2]
Source link