Fasahohin Zamani Na Kasar Sin Sun Bullo Da Sabbin Sassa Na Sayayya
[ad_1]
A yayin taron dandalin Zhongguancun na shekarar 2026 da ya gudana a birnin Beijing kwanan nan, mutane sun shaida al’amura kan yadda fasahar kirkirrarriyar basira ta AI ke karfafa masana’antu daban-daban.
Mahalarta taron dandalin mabambanta sun bayyana wa wakilan CMG cewa bunkasar fasahar kirkirarriyar basira da sauran masana’antu na kasar Sin sun haifar da sabbin bukatun masu sayayya, da kuma kara kuzari a kasuwar sayen kayayyaki. Abin da ya fi samun yabo ma shi ne, maimakon koma bayan da ake samu na farfadowar tattalin arzikin duniya, a ko yaushe kasar Sin tana bin turbar bude kofa a matakin koli game da kimiyya da fasaha, da hadin gwiwa, inda ta zamo ginshiki ga sabbin kirkire-kirkiren fasaha na duniya.
A duniya, rungumar tafiya tare da kasar Sin tana nufin tafiya ko hulda da katafariyar kasuwar sabbin kirkire-kirkiren manhajoji, da samun damarmaki na bunkasa a matakin koli da kuma kyakkyawar makomar gobe. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link