Gwamnatin Tarayya Ta Janye Ƙarar Da Ta Kai Sanata Natasha

[ad_1]

Gwamnatin Tarayyar ta janye tuhumar laifi da ta shigar a kotu kan Sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan. An bayyana hakan ne cikin wata sanarwar janye shari’a da aka shigar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, inda aka nuna an dakatar da dukkan matakan shari’a a kan sanatar.

Takardar janye shari’ar, mai ɗauke da lambar FHC/ABJ/CR/195/2025an sanya mata ranar 12 ga Disamba, 2025, kuma an gabatar da ita bisa tanade-tanaden sashe na 108(1), 108(2)(a) da 108(5) na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka (ACJA), 2015. A cewar takardar, Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya bayyana aniyarsa ta janye shari’ar gaba ɗaya.

  • Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Sanata Natasha
  • Wang Yi: Sin Babban Ginshiki Ce Ga Ci Gaban Duniya Duk Da Matsalolin Da Ake Fuskanta

Takardar ta samu sa hannun Daraktan Gurfanar da Ƙararraki na ƙasa (DPP), M.B. Abubakar, da Aderonke Imana, Mataimakiyar Babbar Lauya ta Jiha, a madadin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi. Rahotannin kotu sun nuna cewa Kotun Tarayya da ke Abuja ta karɓi takardar a ranar 15 ga Disamba, 2025, tare da tabbatar da sahihancinta a ranar 18 ga Disamba, 2025.

A baya dai, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ya umurci lauyoyinsa da su janye dukkan shari’un da ya shigar kan mutane bisa zargin bata masa suna. Wannan na zuwa ne bayan rahoton cewa Akpabio ya shigar da ƙarar ɓata suna ta Naira biliyan 200 a Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja, kan Akpoti-Uduaghan dangane da zargin lalata masa suna da aka yi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *