Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku

[ad_1]



Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin babban abokin gabar ɗan Adam.

Ya ce ƙaruwar talauci a Najeriya na ci gaba da jawo rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro, da rashin fata a tsakanin jama’a.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook domin bikin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya, Atiku, ya ce wannan rana tana tunatar da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen yaƙar talauci

“Talauci ne babban abokin gabar ɗan Adam. Yana haifar da matsaloli kamar rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro da sauransu,” in ji Atiku.

Ya bayyana cewa matsayin Najeriya a jerin ƙasashen da talauci ya fi ƙamari na nuna buƙatar ɗaukar matakan da za su mayar da hankali kan inganta rayuwar jama’a.

“Abin takaici ne samun kanmu cikin ƙasashen da talauci ya yi ƙatutu. Saboda haka ne nake ci gaba da fafutukar ganin an ɗauki matakau waɗanda za su taimaka wajen kawo ƙarshen talauci,” in ji shi.

Atiku, ya kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta jihohi, ƙungiyoyi da shugabannin al’umma da su haɗa kai wajen yaƙar talauci daga tushe, ta yadda kowa zai taka rawa.

“A matakin gwamnati da kuma al’umma, dole ne yaƙin kawar da talauci ta isa kowane gida, unguwa da makaranta, domin a samar wa talakawa mafita,” in ji shi.

A baya-bayan nan, Atiku yana kira da kawo sauye-sauyen tattalin arziƙi da suka haɗa da samar da ayyukan yi, raba albarkatun ƙasa cikin adalci, da inganta ilimi da lafiya.

Atiku na ganin matakan su ne ginshiƙan da za su taimaka wajen kawo ƙarshen talauci a Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *