Matar da aka yi ittifakin ta fi kowa tsufa a duniya ta cika shekara 116
[ad_1]
Tsohuwar nan ’yar asalin Burtaniya da aka yi ittifakin ta fi kowa tsufa a duniya, Ethel Caterham, a ranar Alhamis ta cika shekaru 116 a duniya.
Ta cika shekarun ne ’yan watanni bayan ta karbi kambun daga hannun wanda yake rike da shi a baya, Inah Canabarro Lucas, dan asalin kasar Brazil.
Ana sa ran dattijuwar za ta yi bikin cika shekarun tare da iyalanta a gidan gajiyayyun da take rayuwa a ciki.
A tarihi dai, wata ’yar asalin kasar Faransa mai suna Jeanne Calment ce ta taba rike kambun mafi tsufa a duniya inda ta shekara 122 da kwanaki 164 kafin daga bisani ta rasu a shekara ta 1997, kamar yadda kundin bajinta na Guinness World Records ya tabbatar.
An dai haifi Ethel Caterham ne ranar 21 ga watan Agustan 1909 a kauyen Shipton Bellinger da ke kudancin Ingila, shekaru biyar ke nan kafin yakin duniya na daya.
Gidan da ke kula da ita da ke yankin Surrey ya yaba wa mutanen da suke taya ta murna da yi mata fatan alheri, amma ya sanar da cewa ba za ta yi kowacce irin tattaunawa da kowa ba a bana.
A bara dai lokacin da ta cika shekara 115, an tambaye ta sirrin tsawon ranta, inda ta ce, “Ba na musu ko cacar baki da kowa, kawai ina sauraron mutane ne kuma na yi abin da na fi so”.
Yanzu haka dai tsohuwar na da jikoki uku da tattaba-kunne biyar, kasancewar ’ya’yanta biyu sun riga ta mutuwa, sannan mijinta yam utu a 1976.
Ta daina tuka mota ne kawai lokacin da ta shekara 100.
Tasha
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link