DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta
[ad_1]
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta kama wani matashi mai suna Innocent Chukwuma a Jihar Ribas, bisa zargin yin kira da a yi juyin mulki ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
Masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce DSS ta bi diddigin Chukwuma bayan ya wallafa saƙonnin da ya yi kira ga sojoji su kifar da gwamnatin Nijeriya.
Chukwuma ya wallafa cewa “ana buƙatar a yi juyin mulki a Nijeriya” tare da kira ga ‘yan ƙasa da su goyi bayan dakarun soji.
Makama, ya ce DSS ta kama matashin bayan ta bibiyi rubutunsa a Intanet.
Yanzu yana hannun jami’an tsaro kuma yana taimakawa wajen gudunar da bincike.
An rufe asusunsa na X saboda karya ƙa’idodin dandalin, kuma har yanzu DSS ba ta gurfanar da shi a kotu ba.
[ad_2]
Source link