Abun Fashewa: Gwamnati ta gargaɗi masu haƙar ma’adanai a Zamfara

[ad_1]



Jami’in kula da ma’adanai na ƙasa a Jihar Zamfara, Samuel Abunumah, ya gargaɗi masu haƙar ma’adanai da su guji amfani da abun fashewa ba bisa ƙa’ida ba, saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar.

Ya ce sun damu kan yadda ababen fashewa ke yaɗuwa, musamman ganin cewa ’yan ta’adda na iya samun su cikin sauƙi.

Saboda haka, ya bayyana cewa gwamnati za ta haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da an bi doka

A cewarsa, suna aiki tare da sashen kula da abubuwa masu fashewa na ’yan sanda domin gano ko masu haƙar ma’adanai na da hannu wajen yawaitar fashewar abubuwa.

Abunumah, ya kuma buƙaci masu haƙar ma’adanai su riƙa bin dokoki yadda ya kamata, musamman wajen sarrafa ma’adanai da harkar gwal.

A nasa ɓangaren, kwamishinan muhalli da ma’adanai na jihar, Kasimu Sani Kaura, ya nuna damuwa kan yadda wasu ke amfani da abubuwan fashewar ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce ya zama dole gwamnati ta binciki lamarin domin daƙile amfani da shi ba bisa tsari ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *