An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a Taraba
[ad_1]
Rikici tsakanin bangarori biyu a garin Donga na Jihar Taraba, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a kan limancin masallacin Juma’a na garin.
Bayanai sun nuna baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun jikkata kuma an lalata dukiyoyi.
Rikicin, kamar yadda Aminiya ta gano, ya faru ne a ranar Talata kan limancin masallacin Juma’a na garin da ke gaban fadar Sarkin Donga.
Wata majiya daga garin ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin kungiyoyi biyu na al’ummar Musulmi a garin kan wanda ya kamata ya zama limami na masallacin na Juma’a.
An ce sabanin ya rikide zuwa rikici mai zafi tsakanin bangarorin biyu, wanda ya haifar da mutuwar mutane biyu da kuma jikkatar wasu da dama.
Majiyar ta kara da cewa jami’an tsaro ciki har da sojoji sun isa yankin domin shawo kan halin da ake ciki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai daga wayar ko amsa sakon da wakilinmu ya aike masa ba dangane da lamarin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link