Firaministar Srilanka: Sin Tana More Sakamakon Raya Kasa Tare Da Kasashen Duniya

[ad_1]

Firaministar kasar Srilanka, Harini Amarasuriya, ta yi hira da wakilin CMG a kwanan baya, inda ta ce, yayin da kasar Sin take kokarin raya kai, tana tsayawa kan manufar hadin gwiwa don tabbatar da moriyar dukkan bangarori. A cewarta, kasar Sin tana more sakamakon da ta samu a fannin raya kai tare da sauran kasashe, ta hanyar aiwatar da ayyukan gini, da bayar da fasahohi na zamani.

A cewar Madam Amarasuriya, kasarta ta Srilanka tana daya daga cikin kasashen da suka fara shiga shirin hadin gwiwa na Ziri Daya da Hanya Daya da kasar Sin ta gabatar. Kana yadda kasar Sin ta zuba jari da ba da taimako wajen gina yankin Port City Colombo, da wasu tashoshin jiragen ruwa a kasar Srilanka, ya shaida hadin gwiwar da ake yi bisa shirin Ziri Daya da Hanya Daya, da sakamakon da aka samu. Madam Amarasuriya ta kara da cewa, a kasashe daban daban da suka shiga shirin, Sinawa suna aiwatar da ayyukan gini daban-daban, wadanda ke haifar da alfanu ga al’ummun kasashen, tare da samun dimbin yabo daga gare su.

Haka zalika, Madam Amarasuriya ta ce, ta fuskar aikin kula da al’amuran duniya, kasar Sin ta nuna cikakken goyon baya ga tsarin kasancewar dimbin bangarori masu fada-a-ji a duniya, da zama karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, tana kuma kokarin kare yanayin ciniki mai adalci da ‘yanci. Duk wadannan abubuwan da kasar Sin ta yi, a cewar Madam Amarasuriya, suna da matukar ma’ana ga duniyarmu.

Sa’an nan, lokacin da ta ambaci abun da take ji a zuci dangane da ziyarar da ta yi a kasar Sin a wannan karo, Madam Amarasuriya ta ce, abun da ta gani a kasar Sin ta sa ta fahimtar muhimmancin manufar mayar da moriyar jama’a a gaban komai. A cewarta, tushen manufofin gwamnatin kasar Sin shi ne buri na samar da hidimomi ga jama’a, da kokarin kyautata zaman rayuwarsu. Inda dimbin nasarorin da aka cimma a kasar suka shaida daidaiton turbar da aka zaba. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *