Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo a Najeriya




Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo a faɗin Najeriya yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya rincaɓe.

Tuni dai ita ma Matatar Dangote ta sanar da ƙara farashin man fetur daga naira 774 zuwa naira 874 duk lita, lamarin da ke ƙara tabbatar da damuwa game da tashin farashin fetur a faɗin ƙasar.

Bayanai sun tabbatar cewa an ɗauki matakin ne saboda rashin tabbas da hauhawar farashin man a kasuwannin duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da ke ƙara ƙazanta.

Binciken petroleumprice.ng ya nuna cewa an riga an fara amfani da sabon farashin, wanda zai iya shafar dillalan sayarwa da kuma masu amfani da fetur a ƙasar baki ɗaya.

Ƙarin farashin ya biyo bayan dakatarwar da matatar ta yi kan lodin fetur daga ƙarfe 12 na dare a ranar 2 ga Maris, 2026, sakamakon farashin mai a duniya da ya wuce dala 80 a kan kowanne ganga cikin dare ɗaya.

Masu sayar da fetur a kasuwannin unguwanni sun bayyana fargaba cewa wannan ƙaruwa na iya kawo ƙarancin mai a wasu wurare, musamman a lokutan da ake da yawan buƙata, inda wasu ke ganin cewa hakan na iya ƙara matsaloli ga masu amfani da motoci da kamfanonin sufuri a Najeriya.

Haka zalika, masana tattalin arziki sun yi gargaɗin cewa ƙarin farashin zai iya janyo hauhawar wasu kayan more rayuwa, wanda zai ƙara tsananta halin tattalin arziki ga talakawa da ’yan kasuwa a ƙasar.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *