Manufofin Farfaɗo Da Noma Ne Ya Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa raguwar farashin kayan abinci da ake gani a kasuwanni a ‘yan kwanakin nan, na da nasaba da manufofi da matakan musamman da aka ɗauka domin gyara harkar kasuwa da ƙarfafa samar da abinci a cikin gida.
Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yayin taron majalisar noma ta ƙasa karo na 47 da aka gudanar a Kaduna, ranar Alhamis 6 ga Nuwamba, 2025.
A cewar ministan, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki alƙawarin tabbatar da ikon cin gashin kai a fannin abinci, inda Nijeriya za ta riƙa samar da abincin da ta ke ci, tare da tabbatar da wadatar kayayyaki a farashi mai sauƙi.
Kyari ya bayyana cewa shirin National Agricultural Growth Scheme–Agro-Pocket (NAGS–AP), wanda ake aiwatarwa tare da hadin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka (AfDB) da jihohi, shi ne ginshikin inganta samar da kayayyakin noman da kuma bunkasa amfanin gona.
[ad_2]
Source link