Sirrin Mallakar Miji

[ad_1]

Ki kasance kullum cikin gano abin da mijinki yake so da abin da baya so. Sanin halayen mijinki zai taimaka miki wajen kyautata rayuwar aure.

Ki kula da abin da ke faranta masa rai da abin da ke vata masa rai, kiyi ƙoƙari wajen kiyaye hakan.

Ki kasance marar kwaɗayin abin hannunsa.

Kada ki zama mai matsin lamba ko yawan neman kuɗi da abubuwan da ba lallai ba ne. Maza suna son mace mai haƙuri da wadatar zuci.

  • Jita-jitar Sauya Sheƙa: Gwamna Yusuf Na Ganawar Sirri Da Tinubu A Aso Rock
  • Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Ki kasance cikin tsaftace muhalli, gidanki da jikinki:Tsafta tana da muhimmanci a rayuwar aure. Ki tabbatar da cewa gidanki yana da tsafta, jikinki yana ɗaukar ƙamshi, kuma kayanki suna da kyau da tsabta.

Ki kula da iyayensa, ‘yan uwansa da abokansa

Iyayen miji da danginsa suna da matsayi mai girma. Idan kika girmama su, zai ƙara sonki da girmamaki.

Ki kasance mai tsoron Allah cikin dukkan al’amuranki.

Duk wani abu da kike yi, ki tabbatar da cewa yana cikin tsoron Allah. Wannan yana ƙara albarka da zaman lafiya a aure.

Kada ki zama mai yawan shige-shige na maƙota

Ki nisanci yawan shiga gidajen mutane ko shiga maganganun da ba su shafe ki ba. Hakan yana iya kawo matsala a gidanki.

Ki sani cewa, kece inuwar hutawarsa da jin daɗinsa

Mace ce ke da rawar gani wajen sanya mijinta farin ciki da jin daɗi a cikin gida. Ki zama mai nutsuwa da kwanciyar hankali ga mijinki.

Idan mai mata kika aura, ki yi biyayya ga matarshi

Idan kin zama kishiya, kada kiyi ƙoƙarin raba shi da uwar gidansa. Ki riƙe ‘ya’yansa kamar naki don samun zaman lafiya.

Ki kasance cikin gano wani sabon salo-salo na wasanni a tsakaninku

Ki guji zama mace mai ɗaukar lamarin aure da sauƙi. Ki riƙa kawo sabbin hanyoyi na soyayya da jin dayi tsakaninki da mijinki.

Ki kasance kullum a jikin mijinki, ki dinga nuna masa cewa ke yarinya ce.

Duk da shekarunki, ki riƙa nuna wa mijinki shagwava da soyayya, hakan yana sa soyayya ta ƙara ƙarfi.

Kada ki dinga yin aikin da namiji yake yi ya zama na kullum.

Mace ta fi kyau idan tana da kwarjini da ladabi. Kada ki zama kamar namiji ta hanyar shiga ayyukan da ba naki ba ne.

Kada mijinki ya gano kina da mita ko saurin fushi.

Maza suna gudun mace mai yawan mita da saurin fushi. Ki kasance mai haƙuri da ladabi wajen magance matsalolinki da mijinki.

Kada ki zama mai bayyana sirrinki a social media.

Sirrin aure yana cikin gida, ba wai a yaɗa shi a Facebook, Twitter ko WhatsApp ba. Kiyi hankali kada ki bayyana sirrin mijinki ga ƙawayenki.

Bayanin Matsayin Mace a Aure

Mace tana da matsayi na musamman a cikin aure.Idan tana da hali mai kyau, tana iya mallakar zuciyar mijinta ta hanyar nuna kyautatawa, biyayya, soyayya da tsafta. Abu mafi muhimmanci shi ne mace ta kasance mai tausayi da fahimta, ta riƙa kula da buƙatun mijinta ba tare da yawan mita ba.

Mata su san cewa mazajensu suna buƙatar kulawa, girmamawa da kwanciyar hankali. Idan mace ta kasance mai nutsuwa da biyayya, to za ta mallaki mijinta gaba ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *