HOTUNA: Rahama Sadau ta shirya bikin fina-finan Arewacin Najeriya

[ad_1]



Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta shirya bikin ɗaga darajar fina-finan Arewacin Najeriya.

Jarumar ta ce ta shirya bikin ne domin tallata fina-finan Arewacin Nijeriya domin ɗaga martabar fina-finan da zummar samun karɓuwa a ƙetare.

Rahama Sadau ta bayyana hakan ne a yayin jawabin da ta gabatar a wajen bikin fina-finan da aka gudanar a dandalin Murtala Square da ke Jihar Kaduna.

Manyan jaruman Kannywood da suka yi fice, ciki har da Ali Jiya, Umar M. Shareef, Abdul D One da sauran fitattun ’yan fim, sun halarci taron waɗanda suka fito domin nuna goyon baya ga jarumar.

Haka kuma, Aminiya ta ruwaito cewa, wasu jarumai daga masana’antun fina-finai na ƙetare sun halarci taron.

Da take ci gaba da jawabi, Rahama Sadau ta ce wannan shi ne karo na farko da aka shirya irin wannan bikin a masana’antar Kannywood, da nufin ganin fina-finan Arewacin Nijeriya sun samu karɓuwa a nan cikin gida da ma ƙasashen waje.

Ta ce manufar bikin ita ce ɗaga darajar fina-finan yankin zuwa matakin manyan masana’antun fina-finai na duniya irin su Bollywood, Nollywood da Hollywood.

Jarumar ta ƙara da cewa za a ci gaba da shirya bikin a duk shekara domin ƙara bunƙasa harkar fina-finai a Arewacin Nijeriya.

Ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai da su ci gaba da bayar da gudunmawarsu domin haɓaka da bunƙasa masana’antar fina-finan yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *