Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin
[ad_1]
Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025.
Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC).
Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba.
Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a.
Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja a mita 92.7 zangon FM, inda za ta kawo shirye-shiryen da za su ilmantar, wayar da kai, da kuma bayar da dama ga ‘yan Najeriya su bayyana ra’ayoyinsu kan batutuwa kamar mulki, ci gaba, al’adu da rayuwar yau da kullum.
Trust Radio wani rukuni ne kamfanin Media Trust, wanda suke buga jaridar Daily Trust, waɗanda aka san su kan tsage gaskiya.
Ana gayyatar jama’a a Babban Birnin Tarayya su saurari tashar, domin sauraren batutuwa da aka gina bisa gaskiya da adalci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link