Kasuwar Tikitin Fina Finai Ta Sin A 2025 Ta Zarce Yuan Biliyan 48

[ad_1]


Dandalin Maoyan mai sayar da tikitin kallon fina finai, ya ce kasuwar tikitin kallon fina finai ta kasar Sin, ciki har da tikitin da aka bukaci saye tun kafin lokacin sayarwa a hukumance, ta zarce yuan biliyan 48, kwatankwacin dala biliyan 6.78, a shekarar 2025 da muke ciki.

A cewar hukumar kula da fina finai ta kasar Sin, zuwa yanzu adadin kudin tikitin ya zarce na bara, tana mai cewa kudin da aka samu a 2024, ya zarce yuan biliyan 42.5, kimanin dala biliyan 5.91.

Ta ce fina finai na cikin gida na ci gaba da kankane kasuwar, inda aka samar da 9 daga cikin fina finai 10 dake sahun gaba, a cikin kasar Sin.

Fina finan da suka hada da “Ne Zha 2” da “Detective Chinatown 1900” da “Dead To Rights”, su ne ke matsayin na 3 dake kan gaba.

Tun farkon bana, masana’antar fina finai ta Sin ta fara sauyawa daga mai samun kudi daga tikitin kallon fina finai zuwa mai karin sassan dake samar da kudin shiga. Ta hanyar hada fim da yawon bude ido da shirye shirye kamar na samun rangwamen sayayya daga tikitin kallon fim da aka saya, fina finai sun kara zama wani abu dake inganta kashe kudi da habakar tattalin arziki. (Mai fassara: FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *