’Yan Jarida Da AGILE Sun Ƙulla Haɗin Guiwar Ƙarfafa Ilimin ’Ya’ya Mata A Sakkwato
[ad_1]
Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Correspondents Chapel a Sakkwato ta yi alkawarin karfafa hadin guiwa da shirin inganta ilimin ‘ya’ya mata na AGILE domin fadada wayar da kan al’umma kan shirye- shiryen bunkasa ilimin ‘ya’ya mata.
Kungiyar ta bayyana kudurin ne a yayin ziyarar da shugabannin ta suka kai wa sashen aiwatarwa na shirin AGILE a Sakkwato a ranar Lahadi.
- Ramadan: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci Ga Limamai 40 A Zamfara
- Binciken CGTN: Karin Haraji Mafi Yawa Ya Haifar Da Gibin Ciniki Mafi Girma Kana Manufar Harajin Trump Ta Wargaje
Shugaban kungiyar, Ankeli Emmanuel, ya bayyana cewar sun kai ziyarar ne domin karfafa hadin guiwa tare da fito da muhimmiyar rawar da kungiyar wakilan kafafen yada kabarai ke takawa wajen yayata labaran ci gaba da isar da su a ciki da wajen jiha.
A jawabin shugaban shirin AGILE a Sakkwato, Dakta Mansur Isah Buhari, ya yabawa ‘yan jarida kan ziyarar tare da ba su tabbacin ci gaba da aiki tare domin bunkasa ilimin ‘ya’ya mata a jihar.
Ya ce tasirin shirin AGILE bai tsaya ga samar da gine- gine kadai ba, ya kuma hada da karfafawa al’umma, inganta sakamakon karatu, samar da karin shigar ‘ya’ya mata a makarantun sakandare da kuma karfafawa al’umma mallakar ayyukan ilimi.
[ad_2]
Source link