Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11 da ta tsare a ƙasarta
[ad_1]
Kasar Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya 11 da jirgin da suke ciki na rundunar sojin saman da ta tsare a ƙasarta saboda zargin keta mata sararin samaniya ba bisa ƙa’ida ba.
Sakin nasu ya biyo bayan tattaunawar da wakilan Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, suka gudanar da shugaban mulkin sojin ƙasar.
A makon da ya gabata ne dai ƙasar ta tsare jirgin na Najeriya ƙirar C-130 da ke ɗauke da sojojin su 11.
Tattaunawar dai ta haifar da sakin dukkan mutanen 11 da kuma jirgin nan take.
Daga baya Minista Tuggar ya gana da ’yan Sojin Sama da aka saki domin tabbatar da lafiyarsu.
Wakilan da kuma mutanen yanzu suna kan hanyarsu ta dawowa Nijeriya.
Ministan ya ce Najeriya ta jaddada bin ƙa’idojin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, ta nuna girmamawa ga ikon Burkina Faso, tare da nesanta kanta daga duk wasu zarge-zargen da ba su da tushe na cin zarafi.
Bangarorin biyu sun jaddada ƙalubalen tsaro da suke fuskanta tare da muhimmancin dangantakar ’yan uwantaka a tsakaninsu.
Jirgin sojin na Najeriya dai ya yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso, Burkina Faso, a ranar 8 ga watan Disamba, 2025, saboda matsalar tangarɗar na’ura.
Hukumomin Burkina Faso sun tsare mutanen tare da kwace jirgin, suna zargin shiga sararin samaniyarsu ba tare da izini ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link