Kotun Amurka Ta Yanke Wa Wanda Yayi Yunƙurin Kashe Trump Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai
[ad_1]
Kotun tarayya a Jihar Florida ta yanke wa Ryan Routh, mutumin da aka samu da laifin shirya kashe shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, hukuncin ɗaurewa har abada.
Rahotanni sun ce Alƙaliyar kotun tarayya, Aileen Cannon, ce ta yanke hukuncin a ranar Laraba, bayan da aka same shi da laifi a watan Satumba kan tuhume-tuhume guda biyar. Masu gabatar da ƙara sun sha alwashin neman hukuncin rai-da-rai, suna cewa lamarin barazana ce mai tsanani ga tsaron ƙasa.
- Jama’a Sun Nuna Rashin Gamsuwa Da Donald Trump Yayin Da Ya Cika Shekara Guda a Wa’adin Mulkinsa
- Bayan Shawo Kan Zanga-zanga: Trump Ya Ƙaƙabawa Duk Ƙasar Da Ke Cinikayya Da Iran Haraji
Shaidu a kotu sun nuna cewa Routh ya shafe watanni yana bin diddigin motsin Trump, inda ya ɓuya a filin wasan golf na West Palm Beach a ranar 15 ga Satumba, 2024, ɗauke da bindiga irin ta tsohuwar Tarayyar Soviet. Jami’in US Secret Service ne ya hango shi, lamarin da ya tilasta yi masa harbin gargaɗi, kafin Routh ya tsere.
Daga bisani aka cafke shi bayan wani farar hula ya rubuta lambar motarsa, abin da ya taimaka wa jami’an tsaro gano shi. Bincike ya kuma gano wasiƙar da Routh ya rubuta da hannunsa, inda ya amsa yunkurin kashe Trump, tare da yin tayin kuɗi ga duk wanda zai kammala abin da ya fara, koda yake hukumomi sun ce babu shaidar yana da irin wannan kuɗi da ya ambata.
Alƙaliya Cannon ta tabbatar da hukuncin ɗaurewa har abada, tare da ƙarin hukunci masu tsawo kan sauran laifukan, inda ta rufe shari’ar kusan shekara guda bayan faruwar yunƙurin kisan.
[ad_2]
Source link