Kurmin Wali: An sako musu ibadan da aka sace a Kaduna
[ad_1]
An sako mutanen da aka sace a garin Kurmin Wali da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
An sace mutanen ne da safiyar ranar 18 ga watan Janairu, 2026, yayin da suke tsaka da yin ibada a wasu coci guda uku.
Wani shugaban al’umma a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an sako mutanen a daren ranar Alhamis.
“Tsakanin karfe 11 zuwa 12 na dare, muka samu labarin cewa manyan motoci sun shiga daji. Daga baya kuma wajen ƙarfe 1 zuwa 2 na dare, suka fito da mutanen da aka sace daga yankin Maro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Ba mu san wa ya je ya karɓo su ba. Haka kuma ba mu da tabbacin ko dukkaninsu aka sako, amma an tabbatar mana da cewa an sako su.”
Har yanzu ba a tabbacin ko an biya kuɗin fansa da babura 17 da maharan suka buƙata ba kafin sakin mutanen.
Aminiya ta ruwaito yadda aka sace aƙalla mutum 177 a lokacin harin da aka kai Kurmin Wali.
Daga baya wasu rahotanni sun nuna cewa kusan mutum 80 sun tsere daga hannun maharan da suka sace su.
Dagacin Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar da sakin mutanen tare da gode wa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu.
“Mu ma mun samu labarin a yau cewa an sako su. Muna farin ciki, kuma a halin yanzu suna hannun gwamnati,” in ji shi.
Dan’azumi ya ce waɗanda aka sako sun haɗa da yara, mata da manya, amma bai yi cikakken bayani ba.
Wani jami’in tsaro ma ya tabbatar da sakin mutanen, inda ya ce, “Eh, gaskiya ne. An sako su cikin dare.”
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin Jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link