‘Yansanda Sun Kama Mutane 22, Sun Ƙwato Makamai, Motoci, Da Ƙwayoyi A Faɗin Nijeriya

[ad_1]

Rundunar ‘Yansandan Nijeriya (NPF) ta sanar da kama mutane 22 da ake zargi da aikata muggan laifuka a jihohi da dama, bayan wasu ayyukan tsaro da rundunar tsaro ta musamman (STS) ta gudanar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, ayyukan tsaron sun kai ga kwato makamai, motoci, babura, miyagun kwayoyi, da wasu abubuwa da ake kyautata zaton ana yin amfani da su wajen aikata laifuka.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar (FPRO), CSP Benjamin Hundeyin ya sanya wa hannu, ta ce an kama mutanen ne saboda zargin aikata laifukan da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, satar motoci, zagon ƙasa ga tattalin arziki, sojan gona, da kuma safarar miyagun ƙwayoyi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *